Fitaccen lauyan nan mai rajin kare hakkin dan adam a Najeriya Femi Falana (SAN) ya shawarci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da ya bayar da umarni a biya malaman jami’o’in ƙasar duka albashinsu na wata takwas.
Wasu daga cikin malaman Jami’o’in ne dai suka yi ƙorafin cewa an biya su rabin albashinsu a watan Oktoba, maimakon albashin wata takwas da suka yi alkawari da gwamnati gabanin janye yajin aikin.
To sai a martanin da gwamnatin tarayyar ta yi ta ce ba zai yiwu a biya malaman albasahin aikin da ba su yi ba.
Cikin wata sanarwa, mai magana da yawun Ma’aikatar Ƙwadago, Olajide Oshundun, ya musanta rahotannin da ke cewa gwamnati ba ta yi wa malaman adalci ba.
“An biya su kuɗin aikin da suka yi ne kawai a Oktoba, daga ranar da suka soke yajin aiki,” a cewar sanarwar.
“An ɗauki matakin ne saboda ba zai yiwu a biya su kuɗin aikin da ba su yi ba. Kowa ta kansa yake yi.”