Rikicin APC: Kwamitin Riko Na Cikin Tsaka Mai Wuya

Shugabancin riko na jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni na cikin tsaka mai wuya biyo bayan kiran da wasu manya na jam’iyyar suka yi akan a sallami shugabannin jam’iyyar na wasu jihohi.

Shugaban rikon kwaryar Mai Mala Buni na cikin wani yanayi akan kiran da ƙusoshin jam’iyyar suka yi, musamman akan batun tunɓuƙe shugabannin jam’iyyar na Jihohin Kaduna,Legas da jihar Ribas da Ogun.

Majiyarmu ta “The Nation” ta ruwaito cewar manyan ‘ya’yan jam’iyyar wadanda suka haɗa da Gwamnoni da Ministoci ‘yan Majalisun tarayya duk sun shiga cikin batun inda suke neman Kwamitin riƙon da ya tsoma baki wajen shawo kan rikicin.

Tun bayan kama ragamar shugabancin kwamitin rikon ya karɓi ƙorafe ƙorafe da dama daga wajen ‘ya’yan jam’iyyar wadanda aka musgunamawa.

Wani al’amari ne mai matukar tasiri ga kwamitin rikon jam’iyyar na ganin sun daidaita al’amurra da ɗinke dukkanin ɓarakar data faru cikin jam’iyyar da daidaita komai cikin watanni shida.

Sai gashi tun kafin aje ko’ina Kwamitin na fuskantar matsin lamba daga wasu ƙusoshin jam’iyyar na cewar ya sanya baki cikin rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar a wasu jihohi.

A takaice wadannan ƙusoshin jam’iyyar na neman a rusa shugabannin jam’iyyar na wasu jihohi ne da sake nada sabbi.

A yayin da wasu tuni suka shigar da ƙararraki a gaban Shari’a suna ƙalubalantar sahihancin shugabannin jam’iyyar a wasu jihohin.

Da yawa yawansu ƙorafe ƙorafen nasu na gaban Kwamitin sulhu na jam’iyyar ƙarƙashin Chief Bisi Akande, amma suna cikin gajin haƙurin jiran kwamitin sulhun ya yi aikin nashi suka ɗaga batun zuwa Kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar.

Sai dai kamar yadda rahotanni ke nunawa shugaban kwamitin rikon na bakin ƙoƙarin shi wajen shawo kan matsalolin jam’iyyar, tun a kwanan nan Buni ya gargadi wani minista da cewar ya girmama umarnin shugaban kasa na daidata Jam’iyyar, inda ya bukace shi da yayi kira ga wasu magoya bayan shi sun janye ƙarar da suka shigar a kotu.

Hakazalika kwamitin ya shaidawa wani tsohon gwamna kuma Tsohon Sanata cewar kwamitin ba zai saurari komai daga garesu ba har sai idan sun kirayi magoya bayansu da janye ƙararrakin da suka shigar a gaban Kotu suna ƙalubalantar shugabancin wasu jihohin.

Kwamitin na iyaka bakin ƙoƙari wajen dinke ɓarakar da jam’iyyar ke fama da ita a wasu jihohi domin ganin komai ya daidaita kamar yadda shugaban kasa ya bukata.

Babbar matsalar da Mai Mala Buni ke fuskanta a yanzu ita ce rikicin jihar Ribas inda Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da Sanata Magnus ke takun saƙa akan wanda ke da alhakin jan ragamar jam’iyyar a jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply