Rikicin APC: El Rufa’i Fayemi Da Amaechi Na Da Hannu Dumu-Dumu

Jam’iyyar APC reshen jihar Ondo ta zargi gwamnoni biyu da wani minista daya da sa hannu a rikicin jam’iyyar da ke aukuwar a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ondo, Henry Olatuja, ya zargi gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da takwaransa na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi akan hura wutar rikicin jam’iyyar da ke balbali a jihar da Kasa gabadaya

Olatuna ya ce goma daga cikin ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar na iya kin fitowa zaben fidda gwani da za a yi a ranar 20 ga watan Yuli.

Ya ce hakan za ta kasance ne idan kwamitin rikon kwarya na shugabancin jam’iyyar a matakin kasa suka nace cewa lallai sai an yi amfani da wakilai a zaben fidda gwani a jihar.

A baya mun kawo rahoto cewa a jiya Laraba ne aka tantance gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Gwamnan na cikin ‘yan jam’iyyar APC 12 da ke hankoron samun tikitin tsayawa takara a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba na 2020.

A wani sako da gwamnan jihar ya wallafa kan shafinsa na Facebook, ya yabawa mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar dangane da tsarin tantancewar da suka tanada.

Ya rubuta cewa: “Yanzu haka dai jam’iyyata ta @OfficialAPCNg ta kammala tantance ni. “Mambobin kwamitin sun kasance su na dub

Labarai Makamanta

Leave a Reply