Rikicin Ƙungiyar Lauyoyi: Lauyoyi Sun Nemi A Cire Wa Malami Muƙamin Shi

Lauyoyi sama da 300 a Najeriya su ka neman a tsigewa ministan shari’an Najeriya, Malam Abubakar Malami, mukaminsa na babban Lauya watau SAN.

Jaridar Punch ta ce wadannan lauyoyi sun bukaci a cirewa babban lauyan gwamnatin tarayya mukaminsa na SAN ne a dalilin yunkurin ragewa kungiyar su karfi.

Wani mai suna Izu Aniagu, shi ne ya kirkiro wannan korafi a shafin yanar gizo, inda ya ke kira ga sauran mutane su taya shi kiran a cirewa ministan mukaminsa.

Mista Izu Aniagu ya yi wa wannan korafi taken ‘Sa hannu a cirewa babban lauyan gwamnatin tarayya, AGF, Abubakar Malami, mukamin babban lauyan Najeriya.”

Kungiyar ta nemi Buhari ya binciki Malami SAN Aniagu ya shigar da wannan korafi ne a shafin change.org a cikin karshen makon da ya gabata.

Hakan na zuwa ne bayan Ministan ya yi wasu garambawul a dokokin shari’a na shekarar 2007, inda ya taba wasu daga cikin ikon da aka ba kungiyar Lauyoyi ta NBA.

Izu Aniagu ya ce kwaskwarimar da AGF ya ke yi wa dokokin kasa su na hadari, sannan ya ce Abubakar Malami SAN ya kan sabawa dokokin kotu da dokarsa.

Har ila yau, Izu Aniagu, ya zargi Ministan da kin binciken wasu da ake zargi da laifi. A cewar Aniagu, Malami ya kan kare wasu marasa gaskiya da ke kusa da shi. A dalilin wannan abu da ya kira son kai, Aniagu ya yi kira ga mutane su sa hannu a wannan korafi da ke neman a raba Malami da mukaminsa na babban Lauya, SAN.

Zuwa karfe 8: 00 na ranar Lahadi, Lauyoyi 383 sun sa hannu a wannan korafi inji jaridar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply