Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce sabon shirin ha?a lambar ?an ?asa ta National Identification Number (NIN) da lambar waya zai tallafa wajen gano miyagu a ?asar.
Saboda haka ne ya shawarci ‘yan Najeriya da su shiga a dama da su a shirin, wanda ya ce zai taimaka wajen samar da bayanai na intanet da za su taiamaka wa tsaron ?asa.
Shugaban na magana ne yayin ?addamar da shirin Revised National Identity Policy wato sabon tsarin samar da lambar ?an ?asa a fadarsa da ke Abuja.
“Lambar NIN za ta gyara wasu daga cikin matsalolinmu na tsaro,” in ji shi. “Cikin sau?i za mu san kowane mutum a Najeriya sannan ta taimaka wajen ha?aka tsaro.
“Lambar wata shaida ce ta ?asa, ya kamata ‘yan Najeriya da kuma wa?anda ke da izinin zama su same ta. Da ita mutum zai samu ayyukan gwamnati sannan ta taimaka mana wajen aiwatar da nagartattun ayyuka cikin ?warewa.”
Yayin taron ne Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami ya gabatar wa da Buhari da sauran manyan jami’an gwamnati sabon katin shaidarsu na ?an ?asa mai ?auke da lambar ta NIN.
Ranar Litinin ne ministan ya ?ara wa’adin ha?a NIN da layukan wayar salula zuwa 30 ga watan Yuni.
Al?aluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa mutum miliyan 54 ne suka ha?a lambar tasu da layin waya, abin da ke nufin layin waya kimanin miliyan 200 na da rajista da lambar NIN, a cewar hukumar NCC.