Real Madrid Ta Doke Liverpool A Gasar Nahiyar Turai

Real Madrid ta samu nasarar doke Liverpool da kwallaye 3-1, yayin fafatawar da suka yi a zangon farko na wasan zagayen kwata final a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Real Madrid da ta karbi bakuncin Liverpool a Spain, ta samu nasarar ce daga ‘yan wasanta Vinicius Junior da ya ci 2 da kuma Marco Asensio. Yayin da Mohamed salah ya ci wa Liverpool kwallonta 1.

A bangare guda kuma Manchester City ta samu nasarar doke Borussia Dortmund da 2-1, bayan da suma suka fafata zangon farko na zagayen kwata final a gasar zakarun turan.

Kevin De Bruyne da Phil Foden ne suka ciwa City kwallayen, yayin da Marco Reus ya ciwa Dortmund 1.

A yau Laraba ne kuma za a fafata sauran wasannin zagayen kwata final din na gasar zakarun Turan tsakanin Bayern Munich da Paris Saint-Germain sai kuma FC Porto da Chelsea.

Related posts

Leave a Comment