Rayuwar Jama’ata Na Cikin Hatsari – Gwamnan Neja

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello a ranar Juma’a ya koka wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa mutanen jiharsa na rayuwa cikin bala’i saboda lalacewar tituna da ambaliyar ruwa.

Bello ya bayyana hakan ne a yayin ganawar da ya yi da shugaban kasar a fadarsa da ke Abuja inda ya nemi gwamnatin tarayya ta kawo ma al’ummar jiharsa dauki don yaye musu bala’in da ke adabar su.

Yayin da ya ke magana da ‘yan jarida bayan ganawarsa da shugaban kasar, ya ce rashin kyawun titunan gwamnatin tarayya yana barazana ga rayuwar mutane kuma hakan na iya raba su da sauran sassan kasar.

Gwamnan ya kuma koka kan yadda ambaliyar ruwa a bana ya lalata filaye masu yawa musamman gonakin rake a jihar. Hakan yasa ya yi kira ga shugaban kasar ya taimakawa manoman jihar da ambaliyar ruwan ya tagayyarar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply