Kungiyar Fulani Makiyayan Shanu a Najeriya, Miyetti Allah (MACBAN) ta kai kuka wajen hukumar yan sanda kan yawan kisan da ake yiwa Fulani a yankin Kudancin Najeriya musamman a jihar Anambara.
Kungiyar MACBAN ta ce hare-haren da ake kai wa Fulani Makiyaya a jihar Anambara ya fara wuce gona da iri, inda a kusan kullum ake kashe Fulani kamar Kaji.
Kungiyar ta Miyetti Allah ta ambaci wasu kananan hukumomi hudu da wadannan hare-hare suka fi aukuwa. Sun hada da karamar hukumar Ayamelum, Anambra ta gabas, Orumba ta Kudu da dunukofia.
Shugabannin Miyetti Allah sun kai kukansu ofishin mataimakin Sifeto Janar na yan sanda a Abuja.
A wasikar shugaban Miyyeti Allah na yankin kudu maso yamma, Gidado Siddiki, ya sanya hannu, ya ce an yi rashin rayuka a wadannan hare-hare.
Ya kara da cewa yanzu haka Fulani makiyaya 30 sun bace kuma an nemi shanu 322 ko sama ko ƙasa.
Saboda haka muna kiran neman taimako daga gareku domin dakile asarar rayuka da dukiyoyin jama’ar tamu.