Rasuwar Sarkin Zazzau: Najeriya Ta Yi Babban Rashi – Fadar Shugaban Kasa

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Lahadi ya jagoranci ministoci da manyan jami’an gwamnati zuwa Birnin Zazzau dake jihar Kaduna domin wakiltar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wurin jana’izar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Dr Shehu Idris.

Daga cikin ministocin da suka rufa mishi baya, akwai ministar kudi, kasafi da tattali, Zainab Ahmed, ministan muhalli, Dr. Mahmud Mohammed da ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika.
Hakazalika, daga cikin wakilan shugaban kasan akwai mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu.

Bayan saukar wakilan a makarantar koyon tukin jirgin sama da ke Zaria, wakilan jihar Kaduna wadanda suka samu jagorancin gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai, suka karbesu.

A yayin mika ta’aziyyar shugaban kasan, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya ce, marigayin Sarkin Zazzau ya bautawa kasa, ya bada gudunmawa ta cigaba da ba za’a manta da ita ba.

Ya ce babbar rawar da ya taka wurin gyara da hadin kan ‘yan Najeriya ba za a manta da shi ba, ya kasance Uba kuma shugaba nagari, wanda a har kullum fatan shi ita ce ciyar da jama’ar kasa gaba.

A martaninsa, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya ce jama’ar jihar Kaduna sun yi babban rashi. Ya mika godiyarsa ga shugaban kasar a kan tura wakilansa da yayi domin halartar jana’izar.

Manyan kasa da dama sun aike da ta’aziyya dangane da wannan babban rashi da aka yi.
A saƙon ta’aziyar shi Shugaban gidajen rediyo da talabijin na Liberty Alhaji Tijjani Ramalan ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin wani rashi da ya shafi ƙasa baki ɗaya, wanda har abada ba za’a manta da shi ba.

Shima tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ahmed Maƙarfi ya bayyana rasuwar ta Sarkin Zazzau a matsayin wani rashi da jarrabawa da ta faɗo wa jihar Kaduna, inda yayi addu’ar Allah ya jiƙanshi ya gafarta mishi.

Babban Malamin addinin musulunci Sheikh Dr Ahmad Gumi a sakon ta’aziyar da ya bayar, ya yi addu’ar neman gafara da samun rahama ga marigayi Sarkin, wanda ya bayyana shi a matsayin abin koyi.

Ita ma a sakon ta’aziyar da ta gabatar, tsohuwar shugabar ƙaramar Hukumar Lere kuma tsohuwar ‘yar majalisar dokokin tarayya Hajiya Saudatu Sani, tace wannan rasuwa ta Sarkin na Zazzau ta yi matukar girgizata, sannan ta yi addu’ar neman gafara a gareshi.

Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.
Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma’a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.

Tuni dai aka yi jana’izar shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a birnin Zazzau, muna addu’ar Allah ya jiƙanshi ya gafarta mishi Allahumma amin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply