Rasuwar Sarkin Zazzau: Babban Rashi Ne Ga Ƙasa – Ramalan

An bayyana rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris a matsayin wani gagarumin rashi ba kawai ga jama’ar Masarautar Zazzau ba, sai ga dukkanin jama’ar Najeriya baki ɗaya.

Shugaban Kamfanin Atar Communication masu gidan Talabijin da Rediyo na Liberty da Jaridun Muryar ‘Yanci da Voice Of Liberty Alhaji Tijjani Ramalan ya bayyana hakan a sakon ta’aziyya da ya gabatar na rssuwar mai martaba Sarkin na Zazzau.

Ya kara da cewar a madadin shi da kafatanin ma’aikatan Liberty sun samu labarin rasuwar ne, cikin kidimewa da shiga damuwa, amma babu dabara ko wani karfi sai ga Allah, muna fatan samun kyakkyawar makoma ga mai martaba.

“A fili yake tarihin arewacin Najeriya da ma Najeriya baki ɗaya ba zai cika ba dole sai an ambato irin gudunmawar da mai martaban ya bayar.

Daga ƙarshe Alhaji Tijjani Ramalan ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta zunubansa ya sanya aljannah ce makomar shi da sauran al’ummar Musulmi baki daya.

Labarai Makamanta