Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa rasuwasr mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso Hakimin Madobi ta Jihar Kano.
A sakon da ya aike ranar Juma’a Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Najeriya ta yi rashin daya daga cikin masu sarautar gargajiya dake da mutunci dattijo wanda ya damu da halin da jama’ar ƙasa ke ciki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba za’a iya mantawa da gudunmuwar da mahaifin Kwankwaso ya bada ba wajen hadin kan al’umma da zaman lafiya da haɓakar cigaban ƙasa a tsawon rayuwarsa.
A cewar Buhari, “marigayi Musa Saleh Mutum ne mai kyawun hali, mai tawali’u da saukin kai. “Ina amfani da wannan damar wajen jajantawa tsohon gwamnan jihar Kano, gwamnatin jihar Kano, da masarautar Kano bisa mutuwar hakimin.”
“Allah ya yafe masa kura-kuransa kuma ya azurtashi da Aljannah, Amin,”.
An gudanar da jana’izar makaman Karaye, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso a birnin Kano, an yi jana’izarsa ne a harabar masallacin gidan Rabiu Kwankwaso da ke unguwar Bompai a jihar Kano. Marigayin ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.