An bayyana rasuwar Fitaccen ?an siyasa tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Abdul?adir Balarabe Musa a matsayin wani rashi da ya shafi Najeriya ba Iyalai ko Jihar Kaduna ka?ai ba.
Shugaban Kamfanin Atar Communication masu Gidajen Talabijin na Liberty TV da Rediyo da Jaridun Muryar ‘Yanci da Voice Of Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan ya bayyana hakan, a sakon ta’aziya da ya mi?a na rasuwar Balarabe Musa a shafin sa na Tiwita.
Tijjani Ramalan ya bayyana Marigayi Balarabe Musa a matsayin wani jigo kuma garkuwan talaka wanda rayuwarsa gaba ?aya ya sadaukar da ita ne wajen fafutukar nemawa talakawa ‘yanci da sama musu tsira a rayuwarsu.
“Hakika rasuwar Balarabe Musa rashi ne da ya shafi kowa a Najeriya, rasuwarsa ta haifar da wani wawakeken gi?i da zai yi wahalar cikewa, ina addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta mishi ya sanya Aljannah makoma Allahumma Amin”