Rasuwa: Tinubu Ya Yi Wa Kwankwaso Ta’aziyar Rasuwar Mahaifi

Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta’aziyya bisa rasuwar mahaifinsa, Malam Musa Saleh Kwankwaso Hakimin Madobi.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas Tinubu cikin wasikar ta’aziyya a ranar Litinin a Legas ya bayyana kaduwa bisa rasuwar mahaifin Kwankwaso, Hakimin Madobi, a safiyar ranar Juma’a a Kano yana da shekaru 93 a duniya.

Jagoran na APC, wadda ya bayyana mutuwar hakimin a matsayin abu mai ciwo ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama ya saka masa da aljanna Firdausi, sannan ya yi addu’ar Allah ya bawa wadanda ya bari hakuri.

“Na yi bakin cikin bisa rasuwar mahaifinka kuma Hakiin Madobi a Jihar Kano, Alhaji Musa Sale Kwankwaso. “Rasuwar iyaye abu ne mai ciwo, ko da ko sun tsufa, ba mu taba son rabuwa da su.
Hakan ya faru da ni kuma na san irin yadda abin ke da ciwo,” in ji Tinubu.

Ya ce ya san irin yadda tsohon gwamnan ya shaku da mahaifinsa da irin amfana da ya ke yi daga gare shi. Kazalika, Tinubu ya ce ya zama dole a yi wa Allah godiya cewa mahaifin na tsohon gwamnan ya yi shekaru masu yawa a duniya kuma ya yi wa al’ummarsa da Najeriya hidima.

Har wa yau, ya yi wa Gwamna Abdullahi Ganduje da gwamnati da al’ummar Jihar Kano ta’aziyar rashin dan su mai muhimmanci ya kuma yi addu’ar Allah ya basu ikon jure hakurin rashi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply