Rashin Tunani Ne A Zargi Mulkin Soja Da Taɓarɓarewar Najeriya – Babangida

Tsohon shugaban ƙasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida Mai ritaya ya ce ba ƙaramin rashin tunani bane zai sa ace Shugabanin mulkin soja ne sanadin matsalolin da ke addabar Najeriya.

Tsohon shugaban sojan, mai shekaru 79 ya bayyana hakan ne a cikin hirar da ya yi da gidan talabijin na Channels TV, a ƙarshen makon da muke ciki.

Babangida wanda ya yi mulkin Najeriya daga 1985 zuwa 1993 ya ce ba za a iya dora wa sojoji alhakin wanzar da matsalolin da ke adabar kasar ba domin farar hula ne suka tsara yadda suke son gudanar da harkokin kasar.

“Ba mu kirkiri matsaloli ba. Munyi kokarin kafa turbar yadda sauran gwamnatoci za su ginu a kai. Mafi yawancin ayyukan da aka gudanar har a lokacin demokradiyya, muna da hannu a ciki.

Mun yi kokarin dauko abinda duniya ke yi a wancan lokacin mun kawo kasar mu. “Ina ganin sakarci ne a ce mu muka kirkiri matsalolin.

Hadin gwiwa ne tsakanin sojoji da farar hula. Ku kuka nuna mana yadda abubuwa ke aiki, hukumomin mulki da gwamnatin, dukkansu hakki ne na farar hula.”

Babangida ya ce baya tsamanin za a iya sake yin juyin mulki a Najeriya. “Duk soja mai hankali ba zai so ya jefa kasar cikin matsaloli da takunkumi ba.

Da zarar ka kwace gwamnati, kungiyoyin Afrika da na kasashen waje za su saka ka a gaba. Ba za a amince da duk wani cigaba da za ka kawo ba. Ba zaka iya aiki kai kadai ba,” inji shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply