Rashin Tausayi Ne Ƙarin Farashin Mai Da Lantarki A Yanzu – Ladaja

Hamshakin ‘dan kasuwan nan kuma tsohon ‘dan takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019 da ya gabata, hon Ibrahim Abubakar Ladaja ya bayyana rashin jin dadin sa dangane da karin kudin wutar lantarki da man fetur da gwamnatin tarayya tayi.

Hon Ibrahim ya bayyana cewa ” a irin halin da talakawan kasar nan ke ciki, bai kamata a kara masu kudin wuta ba. Kowa ya san halin da tattalin arzikin duniya ya shiga sakamakon bullar annobar cutar covid 19 daya tsayar da komai wuri daya.

Kasar mu ta shiga halin kunci na tattalin arziki a sakamakon bullar cutar covid 19 wanda hakan yasa komai ya tsaya kusan watanni 6, duk da haka ya kamata ace gwamnati ta duba halin da talakawa suka tsinci kansu ciki sakamakon zaman gida da sukayi ace ta tallafa masu da wani hanyar da zasu samu sauki ba wai ace gwamnatin da talakawa suka zabeta da kyakkyawar zato ba ace itace ke kara tsunduma talakawan cikin damuwar karin kudin wuta dana lantarki a lokaci daya ba.

Alkaluman da hukumar kididdiga ta fitar ya nuna cewa ‘yan Najeriya na cikin matsanancin talauci wanda ya kamata ace gwamnati ta bullo da sabbin dubarun tallafawa marasa karfi ta hanyar basu tallafin basussuka da dauke masu wani nauyi domin samun saukin rayuwa.

A karshe muna kira ga gwamnatin tayayya da ta duba sha’anin tsaron kasar nan domin kawo karshen kalubalen da fannin ke ciki. Idan har za a dinga garkuwa da manyan jami’an tsaro sai an biya kudaden fansa a kasar mu, ai talaka na cikin damuwa. Domin Wanda ake sa ran zasu kareshi daga yan ta’adda kuma sune yanzu ‘yan ta’addan ke farauta akwai matsala sosai.

Hon Ladaja yayi addu’ar samun dauwamanmen zaman lafiya a kasar nan tare da addua’ar Allah yaba shuwagabannin sauke nauyin al’umma dake kansu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply