Rashin Taɓuka Komai: An Yi Zanga-Zangar Kiranye Ga Uba Sani

Ɗumbin mazauna Kaduna ta tsakiya sun gudanar da zanga-zangar lumana a tituna domin neman a dawo da wakiliansu a majalisar dattijai, Sanata Uba Sani.

Ɗaruruwan masu zanga-zangar da suka mamaye wasu titunan birnin Kaduna sun zargi Sanata Sani da rashin nuna kwazo a majalisa.

Taron zanga-zangar, Wanda aka fara da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Juma’a, ta yi farin jini a wurin matasa.

Masu zanga zangar sun fara tattaruwa daga unguwar Rigasa, karamar hukumar Igabi, kafin su dunguma zuwa birnin Kaduna dauke da takardu masu nuna sakon gajiya da Sanata Sani a matsayin wakilinsu.

Daga cikin irin sakonnin da ke jiki takardun da matasan ke dauke da su akwai masu nuna cewa; “bama bukatar Uba Sani”, “Uba Sani ya bamu kunya”, da sauransu.

A cewar wasu daga cikin matasan, sun shirya zanga-zangar ne bayan sun gano cewa Sanata Sani ya toshe duk wata kafar sadarwa da za’a tuntubarsa sannan kuma bai kara komawa mazabarsu ba tun bayan zabensa a 2019.

Kazalika, sun zarge shi da zama dan kallo da dumama kujera a majalisa kafin daga bisani ma ya matsa laya, a daina ganinsa gaba daya a zauren majalisa

Jaridar Daily Nigerian ta ce Sanata Sani bai amsa sakon da ta aika masa domin jin ta bakinsa akan zargin da masu zanga-zangar ke yi masa ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply