?umbin jama’a mazauna Kaduna ta tsakiya sun gudanar da zanga-zangar lumana a tituna domin neman a dawo da wakiliansu a majalisar dattijai, Sanata Uba Sani.
?aruruwan masu zanga-zangar da suka mamaye wasu titunan birnin Kaduna sun zargi Sanata Sani da rashin nuna kwazo a majalisa.
Taron zanga-zangar, Wanda aka fara da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Juma’a, ta yi farin jini a wurin matasa.
Masu zanga zangar sun fara tattaruwa daga unguwar Rigasa, karamar hukumar Igabi, kafin su dunguma zuwa birnin Kaduna dauke da takardu masu nuna sakon gajiya da Sanata Sani a matsayin wakilinsu.
Daga cikin irin sakonnin da ke jiki takardun da matasan ke dauke da su akwai masu nuna cewa; “bama bukatar Uba Sani”, “Uba Sani ya bamu kunya”, da sauransu.
A cewar wasu daga cikin matasan, sun shirya zanga-zangar ne bayan sun gano cewa Sanata Sani ya toshe duk wata kafar sadarwa da za’a tuntubarsa sannan kuma bai kara komawa mazabarsu ba tun bayan zabensa a 2019.
Kazalika, sun zarge shi da zama dan kallo da dumama kujera a majalisa kafin daga bisani ma ya matsa laya, a daina ganinsa gaba daya a zauren majalisa
Jaridar Daily Nigerian ta ce Sanata Sani bai amsa sakon da ta aika masa domin jin ta bakinsa akan zargin da masu zanga-zangar ke yi masa ba.