Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa akwai yiyuwar ayyukan tattalin arziki a Najeriya su tsaya cik sanadin yajin aikin da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC za su tsunduma a ciki daga yau Litinin.
Kokarin da shugabannin Majalisar dokokin kasar suka yi domin sasanta bangarorin ya ci-tura.
Bayan ganawar sa’o’i hudu da shugabannin Majalisar dokokin kasar da yammacin ranar Lahadi a Abuja, shugabannin kungiyar kwadagon sun ce babu gudu babu ja da baya game da yajin aikin gama gari da aka shirya ya fara ranar Litinin 3 ga watan Yuni, 2024.
Sai dai shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ya ce za su tunbi sauran reshoshinsu a kan kiran da shugabannin Majalisar suka yi mu su ma a kan su janye yajin aikin:
“A yanzu ba mu da hurumin janye yajin aikin, yajin aikin zai fara ne yayin da mu mika rokon da shugabbanin Majalisar dokokin kasar suka yi ga rassan mu daban-daban, game da kiran da suka yi a kan mu janye yajin aikin” inji shi.
Tun da farko, Osifo, shugaban kungiyar kwadago (TUC); da takwaransa na kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero; sun gana da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas. a Abuja.
Kungiyoyin kwadagon sun kira yajin aikin ne sakamakon rashin cimma matsaya a tattaunwar da bangarorin biyu ke yi da gwamnatin kasar kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.
Kungiyoyin kwadago fiye da 10 sun yi kira ga ma’aikatansu da su amsa kiran uwar kungiyar kwadago ta kasa har sai abinda hali ya yi.
Ma’aikatan lafiya da bankunan kasuwanci da na sufurin jiragen sama da na sauran fanonin na cikin wadanda za su shiga yajin aiki, abinda ake ganin zai kawo nakasu ga tattalin arzikin kasar.
Kwamared Ibrahim Abubakar Walama , wanda mamba ne a kwamitin zatarwa na kungiyar ta NLC ya shaida wa BBC cewa sun dauki wannan mataki ne saboda tura ta kai bango:
‘’ Duk mun ce za mu shiga yajin aikin gama gari saboda tura ta kai bango ,gwamnati ba ta dauki maganar albashi da muhimanci ba’’
”Yau gwamnati ta ce dubu 60 za a bayar, shin me mutum zai saya da dubu sistin?” in ji shi.
Kwamared Walama ya ce janye tallafin man fetur da na kudin wutar lantarki da gwamnatin kasar ta yi a baya bayan sun kara jefa mutane cikin hali na kaka-ni-kayi
Rahotanni sun ce shugabbanin majalisar dokokin kasar sun shiga tsakani domin kokarin ganin cewa yajin aikin bai gudana ba.
Kungiyoyin kwadagon na NLC da TUC sun ce suna son gwamnati ta yi ‘abinda ya dace ‘ a kan albashi mafi karanci na ma’aikata domin rage mu su radadin tsadar rayuwa.
Gwamnatin Najeriya ta y iwa kungiyoyin kwadogon tayin naira dubu sistin a matsayin albashi mafi karanci sai dai kungiyoyin kwadagon sun yi watsi da tayin inda suka bukaci naira dubu 494
Kungiyoyin sun kuma bukaci gwamnati ta soke karin da ta yi wa farashin wutar lantarkin kasar