Rashin Lafiya Ne Silar Mutuwar Abiola – Abdulsalami

Tsohon Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojan Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya yi hira ta musamman da gidan talabijin na Trust TV, inda ya karyata cewa guba ce ta kashe Mashood Abiola tsohon dan takarar shugabancin kasa a shekarar 1993.

A cewar Abubakar, rashin lafiya ne ya kashe Abiola, akasin abin da ake fada cewa guba aka ba shi a tsare, shekaru biyar bayan ya yi takarar shugaban kasa.

An ruwaito Abdussalami yana cewa ya na dariya saboda akwai rade-radi nan-da-can cewa mu muka hallaka MKO Abiola alhali babu kamshin gaskiya a wannan maganar.

“A duk lokacin da nake magana a kan Marigayi Abiola, ina godewa Ubangiji da ya ba ni dabarar abin da zan yi a sa’ilin da ya bani shugabancin kasar nan.” “A ranar da Moshood Abiola ya cika, Allah ya jikinsa, abubuwa biyu ko uku sun faru da suka sa na ke godewa Ubangiji da ya yi mani jagoranci.”

Na karbi bakuncin tawaga daga kasar Amurka a karkashin jagorancin Pickering, a lokacin yana sakataren gwamnati ko makamancin haka.” “A tawagar zan iya tunawa da kyau akwai Susan Rice. Zan tuna ta sosai saboda rawar da taka daga baya.” “Bayan mun gama tattaunawa za su bar ofishina, sai Pickering ya ce mani “’Yallabai mun nemi mu ga Mashood Abiola, amma an hana mu.’’

‘‘Meyasa aka hana ku? Wanene ya hana ku?’ Nan take na dauki mataki, na ce za ku gana da Abiola, Na fadawa CSO cewa ya hada su da Abiola Allah ya sa a gaban wasu aka yi.

Tsohon shugaban ya ce da farko babu mai ganin Abiola sai likitansa, amma da ya karbi mulki sai ya bada dama ‘yanuwansa su samu damar ganin shi a tsare. Ana irin wannan yanayi da ‘yanuwansa suke ganawa da shi ne sai tawagar Amurkan ta je ta hadu da Abiola, a nan kwatsam sai rashin lafiya ya kama shi.

“A wajen wannan zama da tawagar Amurka sai Abiola ya fara rashin lafiya, nan-take da jami’an tsaro suka kira Likitoci su duba shi, sai aka zarce asibiti.” “Abin bakin-ciki, a asibitin ya rasu. CSO dina ya kira ni, ya fada mani cewa yana da labarin bakin-ciki; ya ce Abiola ya mutu. Abin ya yi matukar girgiza ni.”

Matsalar bayan nan ita ce yadda za a sanar da iyalin marigayin ya mutu, Abdussalami ya ce Babagana Kingibe ya taimaka wajen tattaro iyalin Abiola. Janar Abdussalami ya ce ya shiga ba danginsa hakuri, har Susan Rice ta ce wannan ba aikinsa ba ne, ta shiga lallashin su kafin a sanar da mutuwar ga Duniya.

Related posts

Leave a Comment