Rashin Iya Shugabanci Ne Silar Jefa Najeriya Halin Da Take Ciki – Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce, babu wani ci gaban da aka samu a jihohin kasar da ke karkashin jagorancin mutane masu rike da matsayin farfesa ko dakta da tsoffin sojoji, har ma da malaman makarantu.

Obasanjo ya ce duk da yake an samu wasu jajirtattun shugabannin da ba su da yawa, akasarinsu ba sa iya mulki mai kyau saboda rashin samun mataimaka na gari, abin da ke hana su jagorancin da ake bukata.

Tsohon shugaban ya ce, rashin tattaunawa tsakanin shugabannin da masu taimaka musu, kan haifar da gibi wajen musayar ra’ayi, matakin da ke hana samun fahimtar juna da hadin-kai wajen cimma manufar ci gaba da ake bukata.

Obasanjo ya ce, bayan kwashe shekaru 60 da samun ‘yancin kan Najeriya, har yanzu shugabannin kasar sun kasa samar da yanayin shugabanci mai inganci wanda zai samar wa kasar ci gaba da kuma magance banbance-banbancen da ake samu na kabilanci da addini da kuma shiya.

Tsohon shugaban ya ce, yadda ake tafiyar da dimokiradiyar Najeriya ya haifar da rabe-raben kawuna da mummunar alaka da rashin amince wa juna da kuma rashin kishin kasa a tsakanin jama’a da kuma al’umma a sassan kasar.

Obasanjo ya ce, abin takaici ne yadda karya da zage-zage da son kai suka mamaye yakin neman zaben da ake gudanarwa yanzu haka, maimakon gabatar da shirin da ake da shi na gina kasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply