Rashin Imani Ne Rufe Asusun Jagororin EndSARS – Galadima

Tsohon Aminin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Buba Galadima ya yi watsi da takunkumin da aka sanya wa jagororin masu zanga zangar EndSARS na rufe asusun ajiya na bankunan su.

Babban bankin Najeriya (CBN) ya samu wani umurnin kotu, inda ta umurci wasu bankuna da su rufe asusun mutane 19 da wani kamfani da a ka alakanta da zanga zangar EndSARS kan zargin daukar nauyin ta’addanci.

Da yake magana a lokacin da ya bayyana a shirin Arise TV a ranar Litinin, Galadima ya bukaci Buhari da ya yi umurnin bude asusun bankunan da aka rufe, inda ya bayyana yunkurin a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma rashin imani ne ƙarara, sannan ya tunatar da Shugaban kasar cewa Najeriya na mulkin damokradiyya ne bana sojoji ba.

”Abunda gwamnati ta yi ba daidai bane, bata da ikon hana ‘yan Najeriya tafiya zuwa wajen kasar ko kuma hana su iko da asusun bankunansu, laifin me suka yi da har za’a ɗauki tsattsauran mataki irin wannan a kansu?

“Wadannan matasa sun yi zanga zangar lumana ne a kan hukumomin gwamnati. Me yasa bayan kun lallashe su ko bayan jami’an gwamnati sun far masu ko kashe su, sannan kuka dauki wannan mataki na toshe asusun bankunansu? Wannan baya bisa kundin tsarin mulki.

“Ina aika wannan sakon zuwa ga shugaban kasa imma ya sani ko bai sani ba, a nuna masa abunda na fadi. Mutanensa basu da hakkin yin abunda suke yi.
“Don Allah su janye sannan su bude asusun wadannan matasa sannan su barsu su gudanar da harkokinsu a matsayinsu na ‘yan Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply