Tsohon na hannun daman Shugaban ƙasa Buhari Malam Buba Galadima, ya ce, abin baƙin ciki ne da takaici kuma rashin imani ne ƙarara ɓoye kayayyakin tallafin CORONA da gwamnoni suka yi, kuma tabbas jami’an gwamnatin wata jiha da bai bayyana sunanta ba, sun taba tunkarar ofishinsa domin sayar da kayayyakin tallafin korona da suka karbo daga gwamnatin tarayya.
Dattijon dan siyasar ya caccaki gwamnatocin jihohi a kan boye kayan abincin da ‘yan kasuwa da kungiyoyi (CACOVID) suka bayar a matsayin gudunmawarsu domin tallafawa talakawa lokacin annobar korona.
Galadima ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da aka yi dashi a wani shirin gidan talabijin din AIT da aka watsa kai tsaye ranar Litinin.
“Na san jihar da jami’an gwamnatinta suka boye kayan tallafin korona a manyan shaguna tare da zuwa ofishina domin neman masu sayen irin wadannan kayan. “Har sharadi suka gindaya cewa dole mai siyan kayan ya kasance ya fito daga wata jihar daban,” a cewar Galadima.
Da aka tambayeshi ko ya sanar da jami’an tsaro wannan bayani mai muhimmanci, sai Galadima ya mayar da matani da cewa, “ai ko yanzu haka suna sauraron abinda nake fada. Kar jami’an tsaro su kalli jawabina a matsayin na makiyi, ni dan kasa ne mai kishi da ya sadaukar da rayuwarsa domin fadin gaskiya”.
Galadima ya kara da cewa ya san abinda ya fada zai iya zama sanadin rasa rayuwarsa.
Gwamnoni suna cigaba da shan suka a kan zarginsu da boye kayan tallafin korona da suka karba daga gwamnatin tarayya da wasu kungiyoyi masu zaman kansu.