Gwamnatin Jihar Bauchi tayi fatali da zargin Kungiyar Yan’kwadago ta jihar, kan cewa ta gaza biyan ma’aikata har su 10,000 albashinsu, a cewar kwamishinan kudi Umaru Sanda Adamu su 350 ne, kuma suna da matsaloli dabamdabam ne.
Indai ba a manta ba a ranar litinin ne shugaban kungiyar kwadagon tayi wuf sanar da yan’jarida kan abunda suke cewa ma’aikatan jihar sunyi sallah ba tare damn sun sami albashinsu ba, kuma sunyi korafi amma babu abun da ya chanza.
Kwamared Danjuma Saleh ya kara da cewa lamarin ya shafi mafi yawancin ma’aikatun Gwamnatin jihar.
“Mun fahimci cewar fiye da ma’aikata dubu goma ba su samu albashi na watan Yuli da ya gabata ba. Mun fahimci hakan wani yunkuri ne Gwamnatin jiha na rage yawan ma’aikatanta,” in ji Shugaban kwadago na jihar, Kwamared Danjuma Saleh.
Sabo da haka yace sun yanke shawarar tsunduma cikin yajin aiki in gwamnati bata chanza ba game da biyansu hakkokinsu baki daya ba.
Bugu da kari kungiyar ta yi batun cewa gwamnatin Bauchin ta dauko hayar wani kamfani mai suna (Dynatech System Solutions) domin gyara lamarin biyan albashi a Jihar, inda kungiyar ta ce ban da dagula lamura babu abun da kamfanin tayi, suna masu nuna rashin gamsuwarsu da kamfanin sakamakon rashin kwarewa bisa aikin da gwamnati ta sa suyi.
Har ila yau kungiyar kwadagon ta zargi kwamishinan kananan hukumomin jihar da dagula lamuran na dakatar da wasu ma’aikata da suka kunshi sakatarorin kananan hukumomi, da sakatarorin ilimi hadi da wasu ma’aikatan ba tare da bin matakan da suka dace ba.
Haka nan ta nemi gwamnatin jihar da gaggauta biyan kudaden kungiyoyi na alawus-alawus dinsu cikin hanzari ko kuma su dauki matakan da suka dace.
Sai dai gwamnatin Jihar Bauchi daga bisani ta mai da martani da cewa wasu zarge-zargen duk rashin madafa ne, inda ta ce sam basu hana ma’aikata sama da dubu goma albashinsu ba.
Kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Umaru Sanda Adamu, shine ya maida martanin a madadin gwamnati da cewa alawus na ma’aikatan lafiya da kungiyar ta yi korafi
Kwamishinan ya ce zancen kungiyar na cewar ma’aikata dubu goma ba su samu albashinsu ba babu gaskiya a zancen, yana mai cewa mutum 350 ne kawai ba su samu albashinsu ba, ya kuma ce hakan ma ya faru ne sakamakon rashin gano cikakkun bayanai na ma’aikatan, a cewarshi suna nan suna ci gaba da aikin tantance ma’aikatan, yace duk ma’aikacin zahiri ba za su cinye masa albashinsa ba sam.
RashiKan zargi giratuti kuwa, ya shaida cewar gwamnatinsu tana ware wani kaso da take biyan bashin kudin giratuti tun lokacin da suka hau kan kujerar, mulki don haka ne ya ce yanzu ma suna kan bakarsu na ci gaba da biyan kudaden.
Daga Adamu Shehu Bauchi