Rahotannin dake shigo mana daga garin Maraban Jos dake yankin ?aramar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna na bayyana cewar Maaikatan gidan Rediyon Nagarta sun rufe tashar sakamakon abin da suka kira rashin biyansu albashi na tsawon watanni.
Rahotanni sun bayyana cewar Maaikatan sun fito zanga-zanga tun da sanyin safiyar ranar yau talata domin neman ha??insu tare da nuna adawa da shugabanninin gidan Rediyon.
Hakazalika ma’aikatan sun koka da abin da suka kira ?arfa-karfa da shugabannin gidan Rediyon ke yi ta hanyar sallamar kwararrun Ma’aikata da maye gurbinsu da bara gurbi.
Dukkanin kokarin da wakilimu ya yi domin jin ta bakin shugabannin gidan Rediyon abin ya gagara.
Tashar rediyon mallakin Janar Aliyu Gusau ce da ke a matsakaicin zango. Maaikatan sun yi kiran da a diba bukatunsu.