Rashin Albashi: Ma’aikatan Rediyon Nagarta Kaduna Sun Yi Bore

Rahotannin dake shigo mana daga garin Maraban Jos dake yankin ƙaramar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna na bayyana cewar Ma’aikatan gidan Rediyon Nagarta sun rufe tashar sakamakon abin da suka kira rashin biyansu albashi na tsawon watanni.

Rahotanni sun bayyana cewar Ma’aikatan sun fito zanga-zanga tun da sanyin safiyar ranar yau talata domin neman haƙƙinsu tare da nuna adawa da shugabanninin gidan Rediyon.

Hakazalika ma’aikatan sun koka da abin da suka kira ƙarfa-karfa da shugabannin gidan Rediyon ke yi ta hanyar sallamar kwararrun Ma’aikata da maye gurbinsu da bara gurbi.

Dukkanin kokarin da wakilimu ya yi domin jin ta bakin shugabannin gidan Rediyon abin ya gagara.

Tashar rediyon mallakin Janar Aliyu Gusau ce da ke a matsakaicin zango. Ma’aikatan sun yi kiran da a diba bukatunsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply