Shahararren mawaƙin siyasar nan a Najeriya, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, zai saki sabuwar waƙarsa wacce ya rangaɗawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, domin goge laifin da yan ƙasar ke ganin ya yi musu.
Masoya Buharin dai na ci gaba da tambayar ina aka kwana a kan batun kuɗin da suka tura domin yi wa masoyinsu waƙa.
Waƙar dai za ta zo da sabon salo domin ba irin wacce mawaƙin ya saba yi ce a shekarun baya ba, kamar yadda mawaƙin ya faɗa, ana sa ran sakin sabuwar waƙar nan ba da jimawa ba, kamar yadda wata majiya daga mawaƙin ta bayyanawa sashin hausa na APA.
Idan ba ku manta ba a ƙarshen watan oktoba, a shekarar da ta gabata, mawaƙin ya bayyana cewa “ba zai sake yiwa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari waƙa ba, sai idan masoyan shugaban sun biya shi kuɗin waƙar, inda ya nemi masoya Buharin da su tura masa naira 1,000 ɗai-ɗai kafin ya yi wa shugaban waƙar”.