Rarara Ya Ci Dukan Tsiya A Katsina

Shahararren mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara ya sha da kyar, da shi da Ali Nuhu, Abubakar Mai shadda, Tijjani Asase tare da sauran ma’aikatan da suke aikin shirin wakar Kahutu Rarara mai suna ‘JIHATA’ ta rashin tsaro, wadda wakar tana daukar mintuna 32:22.

Daman sun yi kusan kwana uku 3 a Katsina suna shirye-shiryen daukar wakar, suna zuwa wurare da yawa su dauka sai su wuce wani wurin domin samun wani dandalin na gudanar da shirye-shiryen bidiyon wakar.

Wannan al’amari dai ya faru ne a Central market ta jihar Katsina, inda matasa suka yi musu ayari suna fada musu “‘karya ne ba ma yi, ba ma so, dan yaudara ne, miyar gidansa yake gyarawa ba kare talaka yake ba”.

Nan take wurin ya yamutse, inda Ali Nuhu, Abubakar Mai Shadda, Tijjani Asase da duk ma’aikatan da ake shirin wakar da su suka fara neman hanyar guduwa, duk da suna tare da jami’an tsaro har saida suka fasa musu danjar mota.

Abin mamaki kuma shi ne; duk wanda ya ji wakar da ya yi zai fahimci cewa ya yi wakar ne wadda babu son zuciya ko kuma siyasa, kawai don rashin tsaro, kuma babu dan PDP ko dan APC duk yana nuni ne a kan a taru a samar da tsaro.

Labarai Makamanta

Leave a Reply