Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a wani ?angare na bikin samun ‘yancin-kai, Shugaban ?asa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi a ranar yau Asabar, 1 ga watan Oktoba.
Buhari zai gabatar da jawabin ne da misalin ?arfe 7:00 na safe yayin da Najeriya ke cika shekara 62 da samun ‘yancin-kai daga Turawan Birtaniya.
“Ana umartar gidajen talabijin da rediyo da sauran kafofin labarai na latironi da su jona jawabin daga gidan talabijin na NTA da kuma Rediyo Najeriya,” a cewar wata sanarwa daga fadar shugaban ?asar.
Tun daga farkon makon nan aka ga sojojin Najeriya na shirye-shiryen bikin na ranar Asabar, inda jiragen soja za su dinga wasa a sama da kuma faretin girmamawa.