Fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi ta saki sunayen mata da ta yi wa lakabi da ‘matan Buhari’ a cikin shagulgulan bikin ranar mata na kasa da kasa, wato International Women’s Day, IWD.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa a kowanne ranar 8 ga watan Maris na shekara na ake bikin ranar Mata ta duniya.
Maudu’in ranar matar ta 2021 shine “Fuskantar Manyan ?alubale”.
A sanarwar da kakakin Buhari, Femi Adesina ya fitar a Abuja, ya lissafa mata 50 cikin matan Nijeriya da suke rike da madafun iko a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
A cewar hadimin shugaban kasar, bikin ya bada damar a yi duba kan yadda gwamnatin Buhari ke karrama mata.
Ya ce: “Ga jerin sunayen, ‘Matan da Buhari ya ba mu?ami a gwamnatin shi
Wa?anda suka ha?a da:
- Zainab Ahmed, Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa
- Sadiya Umar Farouq, Ministan Harkokin Agaji da Jin Kai
- Pauline Tallen, Ministan Harkokin Mata
- Mariam Yalwaji Katagum, Karamar ministan Masana’antu, Cinikayya da Saka Hannun Jari
- Sharon Ikeazor, Karamar Ministan Muhalli
- Gbemisola Saraki, Karamar Ministan Sufuri
- Ramatu Tijjani Aliyu, Karamar Ministan Abuja (FCT)
- Folashade Yemi-Esan, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
- Mariam Uwais, Mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa
- Jumoke Oduwole, Mashawarciyar shugaban kasa ta musamman kan masana’antu, cinikayya da saka hannun jari, kuma sakatariyar cibiyar saukaka yin kasuwanci ta shugaban kasa PEBEC.
- Mojisola Adeyeye, Shugaban hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC.
- Hadiza Bala-Usman, Shugaban hukumar tashohin jiragen ruwa na Nigeria, NPA.
- Abike Dabiri–Erewa, Shugaban hukumar yan Nigeria mazauna kasashen ketare
- Chioma Ejikeme, Babban sakatariya na hukumar fansho ta PTAD
- Patience Oniha, Direka janar na Ofishin Kula da Basusuka na Kasa
- Aisha Dahir-Umar, Shugaban hukumar fansho ta kasa
- Jummai A.M. Audi, Shugaban hukumar yi wa dokoki garambawul, (NLRC)
- Yewande Sadiku, Sakataren hukumar inganta saka hannun jari Executive Secretary, (NIPC)
- Gloria Akobundu, Shugaban hukumar hadin gwiwa don cigaban Afirka (NEPAD)
- Nnenna Akajemeli, Shugaban hukumar sauraron korafin abokan hulda, SERVICOM
- Folashade Joseph, Shugaban Hukumar Inshora na Noma, (NAIC)
- Cecilia Gaya, Shugaban kwallejin horar da masu tafiyar da mulki, (ASCON)
- Ronke Sokefun, Shugaban hukumar inshora ta NDIC
- Aishah Ahmad, Mataimakiyar gwamnan babban bankin duniya, (CBN)
- Stella Ojekwe-Onyejeli, Sovereign Investment Authority (NSIA)
- Adejoke Orelope-Adefulire, Babban mataimakiyar shugaban kasa na musamman kan Sustainable Development Goals (SDGs)
- Oge Modie, Babban mataimakiyar shugaban kasa na musamman kan sadarwa na musamman
- Moji Rhodes. Babban mataimakiyar shugaban kasa na musamman kan harkokin cigaba da jin kai
- Toyin Adeniji, Shugaban Kananan Kamfanoni da Bankin Masana’antu, (Oversees the Government Enterprise and Empowerment Programme, GEEP)
- Stella Okotete, Shugaban bankin cigaban kasuwanci, NEXIM Bank
- Omolola Abiola, Edewor, Shugaban Deposit Insurance Corporation (NDIC)
- Imaan Sulaiman-Ibrahim, Shugaban hukumar yaki da fataucin mutane (NAPTIP)
33.Lauretta Onochie, Mataimakiyar shugaban kasa a dandalin sada zumunta kuma zababbiyar kwamishina na INEC
34.Dr. Yosola Akinbi – Babban mashawarciya kan tattalin arziki na kasa (NEC) (Ofishin mataimakin shugaban kasa)
35.Dr. Balikisu Saidu, Babban mataimakiya na musamman kan harkokin shari’a, bincike da ka’idoji, (OVP)
36.Prof. Fatima Waziri-Azi – Babban mataimakiya na musamman, bangaren bin ka’idoji (ofishin mataimakin shugaban kasa)
- Foluso Idumu, Babban mataimakiya na musamman, bangaren gudanar da mulki (ofishin mataimakin shugaban kasa)
38.Lanre Shasore, Babban mataimakiya na musamman fanin tsare-tsare (ofishin mataimakin shugaban kasa)
39.Dr Ebi Awosika, Babban mataimakiya na musamman bangaren tuntubar jama’a (ofishin mataimakin shugaban kasa)
40.Olaolu Beckley, Babban mataimakiya na musamman, ajiye bayanai (ofishin mataimakin shugaban kasa)
41.Edewede Akhidenor, Babban mataimakiya na musamman, bangaren gudanar da mulki (ofishin mataimakin shugaban kasa)
42.Nkoli Anyaoka, Babban mataimakiya na musamman, bangaren gudanar da mulki (ofishin mataimakin shugaban kasa)
43.Dr. Lilian Idiaghe, mataimakiya na musamman, Shari’a (ofishin mataimakin shugaban kasa)
44.Tolani Alli, mataimakiya na musamman, isar da rubutattun sakonni (ofishin mataimakin shugaban kasa)
45.Toyosi Onalapo, mataimakiya na musamman tuntubar jama’a
46.Haijya Halima Bawa, mataimakiya na musamman tuntubar jama’a
47.Nonye Ojekwe, mataimakiya na musamman tuntubar jama’a
48.Koko Iyamusa, mataimakiya na musamman, bangaren gudanarwa (Ofishin mataimakiyar shugaban kasa)
49.Fakorede Omotayo Basirat, mataimakiya na musamman kan ayyuka na musamman
50.Omotayo Rachael Omowunm, mataimakiya na musamman kan harkokin gida da bukukuwa.