Ranar Dimokuradiyya: Tinubu Ya Jadadda Aniyar Gwamnati Na Fitar Da ‘Yan Najeriya Daga Kunci

IMG 20240308 WA0066

A yayin da ya ke jawabin, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa gwamnatinsa na dab da kai karshen maganar sabon mafi ?arancin albashi.,

Ya ce idan komai ya kammala, zai mika wa majalisar tarayyar kasar domin su amince da shi wanda ya ke da yakinin zai zama mafi dacewa ga ma’aikatan.

A cewar shugaban kasar: “Ina sane da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Najeriya. Sama da shekaru ya kamata a gyara tattalin arzikin kasar saboda lalacewa da rashin makoma.

“Tun bayan hawan mu mulki, mun aiwatar da sauye sauye wadanda suka zama tubali ga dorewar tattalin arzikin kasa

“Ko a lokacin da ‘yan kwadago suka shiga yajin aiki kan mafi ?arancin albashi, ba mu takura masu ba, mun kyale su saboda ‘yancin su ne, saboda muna da yakinin yin adalci a gare su.”

Alakar dimokura?iyya da tattalin arziki Shugaban kasar ya ce da ace Najeriya na karkashin ‘yan mulkin mallaka, to ba makawa ‘yan ?wadago ba za su samu fuskar yin yajin aikin ba.

Ya yi nuni da cewa manufar dimokura?iyya a kullum shi ne mutunta ‘yancin kowa, amma ba hakan ne zai sa a sauka daga turbad kundin tsarin mulkin kasar ba.

Tinubu ya sha alwashin farfa?o da tattalin arziki da kuma gabatar da tsare tsare ta yadda za a gina Najeriya ba tare da an kuntatawa wani dan kasar ba.

Related posts

Leave a Comment