Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin tarayya na sane da cewa azumin watan Ramadan mai gabatowa zai zo da kalubale masu tsanani ga akasarin ‘yan Najeriya saboda sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bullo da su.
Ya ce manufofin tattalin arziki da ake ?ullo da su na zuwa da kalubale da matsaloli, wanda zai zama “mafi tsanani ga talakawa.”
Daily Nigerian ta ruwaito cewa,Shettima ya bayyana haka ne a yayin taron lacca karo na 29 na gabanin watan Ramadan da daliban jami’ar Legas suka shirya a Legas.
Shettima, wanda mashawarcinsa na musamman kan harkokin siyasa, Hakeem Baba Ahmed ya wakilta, ya yi kira ga ?an ?asa da su yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da kalubalen da tattalin arzikin kasa a halin yanzu cikin “nutsuwa”.
Ya ce: “Shugabancin Shugaba Tinubu ya gane cewa wannan watan Ramadan zai zo da kalubale masu tsanani ga yawancin ‘yan Najeriya.
“Hanyar zuwa inda muke a yau tana da tsayi kuma tana cike da kalubaloli da kuma kasawa mai ban tausayi don gina babbanlr damarmu.
“Sakamakon abubuwan da suka faru a baya su ne ainihin abubuwan da muke fuskanta a yau, kamar hauhawar tsadar rayuwa da kuma rashin amincewa da yun?urin kawo ci gaba.
“Mu tuna cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala yana jarrabar bayinSa da sauki da kuma kunci, kuma yana rokonmu da mu roke shi ya yaye mana kunci, da horo a lokutan yalwa.
“Muna fatan Allah Ya nuna mana azumin watan Ramadan kuma Ya karbi ibadar mu,” in ji shi.