Ramadan: Gwamnatin Katsina Ta Karya Farashin Hatsi

IMG 20240211 WA0197

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewa a yayin da ake tsadar kayan abinci a Najeriya, gwamnatin Katsina tare da haɗin gwiwar ƙananan hukumomin jihar 34 sun ware sama da Naira biliyan 10 domin saye da bada tallafin hatsi domin rabawa ga marasa galihu a cikin watan Ramadan.

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ne ya tabbatar da hakan a yayin ƙaddamar da kwamitocin a matakin jiha da na ƙananan hukumomi da aka ɗorawa alhakin sa ido kan yadda za a raba kayan a ranar Asabar.A cewar sa, shirin na nufin ciyar da mutane kimanin 72,200 a kullum a cikin watan Ramadan.

Hakan a cewarsa, yana nuna cewa samar da tallafin abinci ga mutane kusan miliyan 2.1 (2,166,000) a tsawon lokacin watan azumin.

Sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, ta ce shirin ya kuma haɗa da rage farashin masara, gero, da dawa zuwa Naira 20,000 kan kowane buhu. Domin tabbatar da adalci, gwamnatin ta tsara sayar da kayan hatsin ga mutum biyar duk buhu ɗaya.

Baya ga rage farashin kayan abinci a kan Naira 20,000 kowane buhu, ga kimanin gidaje 400,000, Gwamna Radda ya ce iyalai 33,000 da aka zaɓa daga sassa daban-daban na jihar za su samu kayan abinci kyauta da wasu kuɗaɗe.

Labarai Makamanta

Leave a Reply