Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’ad Abubakar III dake birnin Sokoto, ta umarci al’ummar musulman ?asar nan da su fara neman jinjirin watan Ramadana na shekarar 1442AH daga ranar yau Litinin.
Majalisar Sarkin Musulmin ta bada wannan umarnin ne a ranar Lahadi a cikin wani sa?o da shugaban kwamitin shawara kan al’amuran addinin Musulunci, Sambo Junaidu, ya fitar.
Shugaban kwamitin ya bayyana sa?on Sarkin kamar haka: “Wannan sanarwar na umurtar ?aukacin al’ummar musulmi cewa ranar litinin,12 ga watan Afrilu, 2021 wanda ya zo dai-dai da 29 ga watan Sha’ban, 1442AH, ita ce ranar da za’a fara neman jinjirin watan Ramadana na shekarar 1442AH.”
“Saboda haka ana umurtar musulmi da su fara neman jinjirin watan daga ranar Litinin kuma sukai rahoto idan sun ganshi.” “Ana umartar duk wnda ya ga watan da ya kai rahotonsa ga shugaban ?auyensu don isar da sa?on ga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi”.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya kuma yi addu’ar Allah ya taimaki musulmai gaba ?aya wajen sauke nauyin da ya ?ora musu na yin azumin wata ?aya (Ramadan) ya amshi ibadunsu.
Daga ?arshe Malam Junaidu ya kuma bada lambobin wayan da za’a kai rahoton ganin jinjirin watan kai tsaye zuwa ga kwamitin ganin Watan. Lambobin wayan sun ha?a da: 08037157100, 07067416900, 08066303077, 08036149757, 08035965322 da kuma 08035945903.