An bayyana cewar matakin da gwamnatin jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Nasiru Ahmad El Rufa’i ta dauka na rage adadin yawan Hakimai da Dagatai da sauran masu rike da sarautun gargajiya a jihar ya taimaka wajen ?ara matsalar tsaro a jihar musamman a yankin ?aramar Hukumar Birnin Gwari.
?an Masanin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Idris Abdul-Ra’uf ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Liberty Abuja ya yi dashi a cikin shirin Tambihi a karshen mako.
Basaraken ya ?ara da cewar a baya can lokacin da ake da yalwa ta Hakimai da sauran masu rike da sarautun gargajiya a yankin, ana samun nasara wajen samun isassun bayanai da ke taimakawa jami’an tsaro, hakazalika ana samun ainihin adadin wadanda Iftila’i ya fa?a musu, sa?anin yanzu da komai ya ?ara dagulewa.
?an Masanin na Birnin Gwari ya ?ara da cewar a bisa ga alkaluma dake a hannusu dangane da fitinar dake addabar jama’ar Birnin Gwari, na nuna cewa an kashe mutane sama da 264 da kuma yin garkuwa da mutane 1087 a shekarar da ta gabata.
Idris Abdul-Ra’uf ya ?ara da cewar nauyi ne dake rataye a wuyan gwamnati ta ?ara inganta jami’an tsaro da kayayyakin aiki da kulawa da bukatun su yadda ya kamata ta yadda za su samu damar tunkarar ‘yan ta’adda.
” Dajin Rugu ya ha?a Jihohi da dama kamar Kaduna, Katsina Sokoto Zamfara ya mi?a ya shiga har Nijar ya lankwaso zuwa Jihohin Binuwai da Taraba, saboda haka akwai bu?atar yin aiki tare tsakanin wadannan jihohi domin samun nasara”.
Idris Abdul-Ra’uf ya kuma bayyana salon ya?in da ‘yan Bindiga ke amfani da shi a matsayin salon ya?i ne na sunkuru wanda dole a yi karatun ta natsu, domin samun galaba akai, domin bincike ya nuna wadannan ‘yan Bindiga suna da masu daukar nauyin su a cikin gari da kuma masu basu bayanan sirri.