Rage Radadi: Tinubu Ya Bukaci A Sake Nazari Kan Tallafin Dubu Takwas-Takwas

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci da a yi duban tsanaki kan batun bai wa ‘yan kasar mutum miliyan 12 tallafin naira dubu takwas kowanne a tsawon watanni shida domin rage radadin janye tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Dele Alake ya fitar, shugaba Tinubu ya ce a sake yi wa tsarin garanbawul kasancewar gwamnatin mai sauraron koken al’umma ce bisa la’akari da yadda ‘yan kasar suka yi ca a kan al’amarin.

Wannan ya zo ne sa’o’i bayan Babbar ƙunigyar ƙwadago sunyi watsi da matakin Shugaba Tinubu na neman amincewar majalisar dokoki don karbar rancen naira biliyan 500 daga Bankin Duniya da nufin aiwatar da shirin da ta kira na bogi don rage raɗaɗin ƙarin farashin man fetur.

Ƙungiyar ƙwadagon dai sun ƙara da cewa hakan na nufin gwamnati na neman hanyoyin da za ta sace dukiyar talakawa ‘yan Najeriya, su kuma masu kuɗi su ƙara kuɗancewa.

To sai dai Tinubu ya ce yanzu haka za a fayyace wa ‘yan kasar dukkanin abubuwan da gwamnatin ke Shirin yi wa ‘yan kasar a zuwan tallafin tunda ba batun kudin ba ne kawai.

Shugaba Bola Ahmed ya bayar da umarnin sakin takin zamani da hatsi ga manoma da magidanta kimanin miliyan 50 a dukkanin jihohin kasar 36 da Abuja.

Bugu da kari shugaba Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa za a yi amfani da naira biliyan 500 da majalisar dokokin kasar ta sahhale wa bangaren zartarwa domin rage radadin janye tallafin mai ta hanyar da ta dace.

Inda ya kara da cewa ‘yan Najeriya za su amfana da tsarin ba tare da la’akari da addini ko kabila ko kuma siyasarsu ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply