Rage Radadi: Tallafin Dubu Dari-Dari Ba Zai Wadaci ‘Yan Najeriya Ba – Ramalan

An bayyana cewa ko kaɗan tallafin rage radadin tsadar rayuwa na Naira dubu takwas-takwas da gwamnatin Tinubu ke aniyar aiwatarwa sakamakon janye tallafin mai ba zai wadaci jama’ar Najeriya ba ko da Naira dubu ɗari ɗari ta raba.

Shugaban Kamfanin ATTAR Communications mamallakan gidajen talabijin da rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a birnin tarayya Abuja.

Ramalan wanda tsohon shugaban tuntuba ne na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ya shawarci shugaban kasa Tinubu da cewar maimakon haka kamata ya yi ya mayar da hankali wajen daƙile satar da sauran ayyukan dake gurgunta cigaban Najeriya domin tsamar da ‘yan kasar daga halin kunci da suke ciki.

“Lokaci ya yi da ya kamata a zauna a lalubo hanyoyin da za su kai Najeriya gaba ta hanyar bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma Inganta ci maka ta abinci da samar da tsaro”.

Ya ƙara da cewar kayayyakin tallafin da aka raba a gwamnatin da ta gabata bai ƙara wa ‘yan Najeriya komai ba sai ƙarin talauci saboda haka wannan shirin ma da ake ƙoƙarin yi babu wani alfanu da zai bayar.

Ahmad Tijjani Ramalan ya ƙara da cewar a halin da ake ciki yanzu idan gwamnatin Tinubu ta raba wa’yan Najeriya naira dubu ɗari ɗari ba zai kashe musu ƙishirwar talaucin da suke ciki ba na tsadar rayuwa.

Ya shawarci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen inganta harkar samar da abinci ga ‘yan ƙasa,ilimi da kiwon lafiya da samar da ingantaccen tsaro a kasa gaba daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply