An bayyana yunƙurin Gwamnatin Jihar Katsina na raba Gidaje da Shaguna gami da gonaki ga tubabbun ‘yan Bindiga a matsayin rashin sanin ya kamata, wauta da babban ganganci.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin Garin Kaduna Dr Mahadi Shehu, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna.
Mahadi Shehu ya ƙara da cewar gwamnatin ta Katsina ta nuna halin ko in kula da rashin tausayi ga talakawan jihar, waɗanda suka fito ƙwai da ƙwarƙwata suka zaɓe su, ta hanyar gaza tsare rayuka da dukiyoyin su, amma sai gashi saboda wauta da rafkana, an zo ana yunkurin ba waɗannan ‘yan Bindiga Gidaje da Shaguna, a inda suka yi ta’addanci.
“Yanzu a jihar Katsina da akwai Mata sama da 4000 wadanda aka jefasu Zawarcin dole sakamakon karkashe mazan su da aka yi, akwai yara marayu sama da 32,000 waɗanda ke rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira, amma Gwamnatin Jihar Katsina ba ta kalli wannan al’amari ba, sai ta ɓuge da batun ba waɗanda suka jefa waɗannan mutane cikin bala’i kayan alatu, wanda wannan ƙarfafa gwiwa ne ga’yan Bindiga su cigaba da ta’addanci”.
Mahadi Shehu ya bayyana cewar yin sulhu da ‘yan ta’adda abu ne mai kyau, to amma ana yin shine bisa ga tsari da ilimi ba bisa jahilci kamar yadda gwamnatin Katsina ta yi ba, domin kawai a samu hanyar da za’a saci dukiyar jama’a.
Daga ƙarshe ɗan kasuwar wanda shima ɗan asalin jihar Katsina ne, ya tunatar da Gwamnan jihar Masari da Sakataren Gwamnatin jiha Mustafa Inuwa, su tuna Alkawurran da suka ɗauka lokacin shiga fadar gwamnati sannan su tuna cewa za’a mutu gaba daya a tsaya gaban Ubangiji, saboda haka su shiga taitayinsu domin akwai ranar ƙin dillanci.