Rabin Albashi: ASUU Ta Yi Barazanar Sake Tsunduma Yajin Aiki

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar malaman jami’a (ASUU) ta yi wata kwarya-kwaryar zanga-zanga kan rikicinta da gwamnatin tarayya da kuma rashin biyansu cikakken albashi a watan da ya gabata.

ASUU ta ce wannan zanga-zanga sun yi ta ne don nuna damuwa ga yadda ake yiwa Malaman rikon sakainar kashi da kuma alanta tsarin ‘ba aiki ba albashi a kansu’, da kuma tursasa su su koma bakin aiki ba tare da samun hakkinsu ba.

Kungiyar ta ce, matukar gwamnati ta gaza biya musu bukata, to tabbas majalisar zartaswarta za su koma su sake zama tare daukar matakin da ya dace cikin gaggawa.

Da yake jagorantar gangamin zanga-zangar a farfajiyar jami’ar Abuja, shugaban ASUU na yanki, Kassim Umaru ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su takura gwamnatin tarayya ta biyawa kungiyar bukatunta.

ASUU ta kuma yi kira ga shugaban majalisar wakilai ta kasa, Femi Gbajabiamila da ya cika alkawarin da ya shiga tsakaninsa da kungiyar, Hakazalika, kungiyar ta bayyana cewa, ba za ta hakura kan bukatarta ba har sai gwamnati ta biya su kudaden da suke binta tun daga 2020 zuwa yanzu kamar yadda yake a yarjejeniya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply