Qatar Ta Bada Tallafin Dala Dubu 50 Ga ‘Yan Gudun Hijira

?asar Qatar ta bada tallafin dala dubu 50 don gina wa yan gudun Hijira makaranta a sansaninsu na Wassa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Jakadan kasar a Nijeriya Mubarak Almuhannadi ya bayyana bada gudunmuwar, ranar Talata a Abuja, lokacin da babban Kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun Hijira ta Nijeriya Sanata Basheer Muhammad suka kai masa ziyara.

Almuhannadi, ya ce dalilin bada gudunmuwar shi ne don taimakon ayyukan hukumar, na tallafa wa ‘yan gudun hijirar.

A na sa bangaren, shugaban hukumar ya godewa kasar kan wannan tallafi, tare da bada tabbacin hukumar za tayi amfani da ku?in bisa amana.

Ta’addancin ?ungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya jefa jama’a da dama barin gidajen su da fa?awa gudun hijira a ?asashe makwabta.

Related posts

Leave a Comment