Peter Obi Bai Cancanci Zama Shugaban Kasa Ba – Adams Oshiomhole

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, da kasancewa babban mai kawo rashin ayyukan yi a Najeriya, wanda bai cancanci ya zama shugaban ƙasa ba.

Oshiomhole yayin jawabinsa wurin kaddamar da kamfen dinsa na neman kujerar sanata na mazabar Edo ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC ya ce Obi ya bada gudunmawa wurin rashin aikin yi a kasar kasancewarsa mai shigo da kayan masarufi daga kasashen waje.

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya ce kasancewar Obi ne ke da kanti mafi girma a Abuja wanda ke siyo tufafi da wasu kayayyaki daga kasar waje, shi (Obi) yana bada gudunmawa wurin karya darajar naira, da jefa matasa cikin matsalar rashin aikin yi.

“Obi ke da kanti mafi girma a Abuja kuma duk kayan da aka sayarwa a wurin daga kasashen waje aka shigo da su, don haka idan yana sayar da abubuwa na kasar waje, tufafi da wasu kayayyakin, yana bada gudumawa kan dalilin da yasa Najeriya ke kasa saboda yana samar da aiki a kasar waje kuma yana shigo da rashin aikin yi Najeriya.”

Peter Obi dan kasuwa ne kuma ya rike mukamin shugaba a daya cikin bankunan zamani a Najeriya. Shine kuma mammalakin fitaccen kantin Next Cash and Carry da ke Jabi a Abuja, babban birnin tarayya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply