PDP Ta Gargaɗi Mai Mala Buni Akan Yawan Sukan Gwamnonin Jam’iyyar

Jam’iyyar adawa ta PDP ta gargadi gwamnan jihar Yobe kuma Shugaban rikon kwarya na jam’ iyya mai mulki ta APC Mai Mala Buni da ya daina zagin gwamnoninta.

Babbar jam’iyyar adawar ta bayyana hakan ne a a shafinta na Twitter a ranar 4 ga watan Oktoba, ta gargadi gwamnan da ya daina aiko wasu mutane a APC domin su zagi gwamnoni da sauran shugabanninsu don kawai su janye hankalin mutane daga gazawa da matsalolin jam’iyyar mai mulki.

Jam’iyyar adawar ta yi kira ga Buni da ya tsara hanyar da ta fi dacewa domin magance gazawar APC a matakan jiha da tarayya.

Ta ce mafita zai nema maimakon kokarin amfani da wasu mutane da ba a san da zamansu ba wajen cin zarafin gwamnoni masu kokari.

PDP ta ci gaba da cewa gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwarta sun fi kokari ta kowani fannin, fiye da takwarorinsu na APC.

A gefe guda, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi martani a kan yawan rikici da ake ta samu yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamnan Ondo.

Babbar jam’iyyar adawar ta yi ikirarin cewa jam’iyyar APC na aiki tare da Gwamna Rotimi Akeredolu domin razana dan takararta, Jegede Eyitayo da mutanen jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply