PDP Ta Garga?i Sabon Shugaban Hukumar EFCC

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bu?aci sabon Shugaban hukumar ya?i da masu yi wa tattalin arzi?in ?asa zagon ?asa EFCC Abdulrasheed Bawa da ya kula sosai wajen dawo wa hukumar martabarta ta asali.

Jam’iyyar ta shawarci Bawa da ya kaucewa maimaita kuskuren da tsohon Shugaban Hukumar Ibrahim Magu ya yi ta hanyar gujewa shiga siyasa ko ba da damar amfani da hukumar domin musgunawa ko tauye ?anci ko domin azurta kai kamar “yadda ya faru da shugabanta da ya gabata.”

A wani jawabi ta bakin kakin Jam’iyyar ta PDP, Kola Ologbondiyan, a rannar Asabar, ya bayyana cewa wa?ancan abubuwa su ne suka lalata ?warewar hukumar EFFC da kuma jirkita ayyukanta da sa mutane yanke ?auna da cewa za ta tabbatar da adalci da kuma tafi da ayyukan ta yadda ya kamata.

“Muna tuna wa sabon shugaban hukumar EFCC cewa PDP ce ta kafa wannan hukuma ta ya?i da cin-hanci da rashawa, amma ba a matsayin wata hanya ta cin zali da firgita ?an Najeriya da ba su ji ba su gani saboda dalilai na siyasa da kuma dalilai na ?ashin-kai.”

Sannan ya cigaba da cewa, “PDP ta lura cewa sabon shugaban ya samu horo daga ?wararru a hukumar wanda hakan ya sa ?an Najeriya sa ran zai yi amfani da horon da ya samu wajen gyara tsarin aiki da dawo da martabarta daidai da na ?asashen ?etare.”

“Har’ila yau, Jam’iyyarmu na kira ga shugaban na EFCC cewa, ta la’akari da shekarunsa da horansa, ya kamata ya nuna kyakkyawan misali ga ?an baya wajen sakawa ?an Najeriya saboda ?arfin guiwar da suke da shi a kan sa.”

Related posts

Leave a Comment