PDP Na Da Sauran Lokacin Sulhu Da G5 Kafin Lokaci Ya Kure – Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba gwamnonin G-5 zasu kulle duk wata damar tattaunawar neman sulhu a jam’iyyar PDP.

Tun bayan kammala zaben fidda gwanin dan takarar shugaban, babbar jam’iyar hamayya ta rasa zaman lafiya a cikin ta kan kiraye-kirayen cire Iyorchia Ayu, ko ya yi murabus daga shugaban jam’iyya.

Kiran wanda Gwamna Wike da yan tawagarsa ke kan gaba, sun ce ba zai yuwu dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya na kasa su fito daga yanki ɗaya ba.

A wata hira da BBC ranar Jumu’a, gwamna Wike yace ba gudu ba ja da baya matukar aka kai matakin da G-5 ta bayyana dan takarar shugaban ƙasan da zata marawa baya.

“Abinda nake son faɗa maku shi ne ya kamata PDP ta yi amfani da damarta saboda akwai lokacin da zamu rufe kofa kuma ba abinda zai faru, idan lokacin ya yi ko sama zata faɗo sai dai ta fado.”

“Ba wanda zai wa ɗayanmu barazana, idan muka yanke hukunci ba zamu goyi bayan dan takarar PDP ba muna da hujja zamu bayyana dalilanmu kuma babu wanda zai iya wani abu, ya kamata su kula.” Mu yan siyasa ne muna da dabaru.

Labarai Makamanta

Leave a Reply