PDP Ce Mafita Ga ‘Yan Najeriya – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, kuma ?an takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP a za?en da ya gabata Alhaji Atiku Abubakar, ya ce PDP ce ta dace da ‘yan Najeriya, kuma ya tabbata a fili cewa PDP alheri ce ga Najeriya.

Wazirin na Adamawa Atiku ya ?ara da cewar PDP ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 16 cikin natsuwa da kwanciyar hankali kafin APC ta amshi mulkin Najeriya a 2015, ta jefa Najeriya cikin halin tsaka mai wuya.

Atiku ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Twitter, inda yace, “PDP ce ka?ai hanyar mafita ga ‘Yan Najeriya, duk bangarorin Najeriya suna bukatar jam’iyyar da za ta gyara Najeriya, ba wacce za ta lalata ta ba.

“Jam’iyyar PDP ta tabbatar da za ta gyara Najeriya, sannan ina rokon ‘yan Najeriya da su amince da jam’iyyar don za ta tabbatar da adalci ga kowa.

Related posts

Leave a Comment