Osinbajo Ya Wakilci Buhari A Taron ECOWAS

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Oisnbajo ya tafi Accra babban birnin ƙasar Ghana domin wakiltar Shugaba Muhammadu Buhari a wani taro na musamman da Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta shirya.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar Laolu Akande ne ya fitar da sanarwar inda ya ce shugabannin ƙasashen yammacin Afrika za su tattauna a yayin taron kan batun siyasar ƙasar Mali.

Osinbajon ya tafi tare da ƙaramin ministan harkokin waje na Najeriya Ambasada Zubairu Dada, haka kuma ana sa ran za su dawo a yau Lahadi.

Ko a Nuwambar bara sai da Mista Osinbajo ya je Accra domin tattaunawa kan wannan batu na siyasar Mali da kuma ƙasar Guinea.

Daga bisani kuma mai shiga tsakani na ƙungiyar ta ECOWAS Goodluck Jonathan ya tafi Mali a ranar 5 ga watan Janairun 2022 domin tattaunawa da hukumomin ƙasar Mali kan batun jadawalin miƙa mulki ga farar hula.

A yau ne gwamnatin sojin ta Mali ta ce ta miƙa sabon jadawalin ga ƙungiyar ta ECOWAS gabannin soma taronta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply