Nuna Tsiraici: Kannywood Za Ta Hukunta Rahama Sadau

Hukumar Ladabtarwa ta masana’antar shirya fina-finan Hausa Kannywood sun shelanta cewar zasu dauki Mataki a kan Jaruma Rahma Sadau.

Yau Litinin da misalin karfe 4:25pm shafin KANNYWOOD ya wallafa sakon a shafin sa kamar haka….

“Zamu Iya kokarin mu domin daukan mataki akanta kuma muna kira ga masoya #kannywood dasu daina yi mata comments ko like idan ta saki irin wannan.
Ku ma da kanku masu kallo zaku iya bamu gudunmawa wajen ladabtar da ita idan zakuyi unfollowing dinta a Instagram/Facebook da shafin Youtube”

A daren Jiya Lahadi ne Jaruma Rahma Sadau ta wallafa wadansu zafafan Hotuna a shafinta na Instagram wanda suka jawo cece-kuce tun daga daren Jiya zuwa yau Litinin.

An ruwaito cewar masanaantar ta Kannywood tayi Amai ta lashe ne don su ma sun wallafa hotunan a shafin su, yanzu kuma sun zo suna Allah wadai.

Wannan bashi bane karo na farko da Jaruma Rahma Sadau take jawowa kanta maganganu marasa dadi, don har yanzu ba’a dauki dogon lokaci ba da Masaantar ta Kannywood ta yafe mata laifukan ta.

Related posts

Leave a Comment