Babban Bankin kasa wato CBN, Karkashin jagorancin Shugaban bankin Mista Godwin Emefele, ya karrama kamfanin Bizi Mobile Cashless Consultant limited da lambar yabo a matsayin gwarzon kamfani mafi jajircewa da kwazo akan tallata shirin e-Naira a daukacin kasar baki daya.
An shirya bikin karramawar da kuma kaddamar da sabon shirin Babban bankin kasa (CBN) mai taken ‘Digital currency (CBDC) e-Naira.’ wanda ya guda a dakin taro na Eko hotel dake Jihar lagos.
A yayin da Shugaban Babban bankin kasa CBN, Mista Godwin Emefel, yake mika kambun lambar yabo ga Shugaban kamfanin Bizi Mobile Cashless Consultant limited, High Chief Dakta Aminu Bizi. Ya bayyana cewa, kamfanin Bizi Mobile shi ne kamfanin da yafi kowanne kamfani jajircewa da nuna kwazo wajen tallata shirin e-Naira ga daukacin Yan Nigeria baki daya.
A nasa jawabin ga manema labarai, jim kadan bayan ya amsa kambun lambar yabon, Shugaban Rukunonin Kamfanin Bizi Mobile Cashless Consultant limited, Alhaji Dakta Aminu Bizi, ya bayyana cewa, “Ina mika godiya na ga Allah da ya nuna mun wannan rana da Babban bankin kasa (CBN) ya zakulo ni, ya karamani da lambar yabo a matsayin gwarzon kamfani mafi jajircewa da nuna kwazo wajen tallata shirin e-Naira a daukacin kasar nan gaba daya. Gaskiya wannan ba karamin abin farin ciki da nuna godiya ga Allah bane.”
Dakta Aminu Bizi ya kara da bayyana cewa, ” tabbas na yarda da maganar da bahaushe ke cewa, ‘bayan wuya akwai dadi na nan zuwa’ tabbas a shekarun baya mun sha wahala sosai wajen tallata duk wani shiri da Babban bankin kasa CBN ya kawo domin ci gaban Yan kasar nan baki daya. Misalin tun daga harkar cashless policy, POS, da kuma shirin e-Naira na kwananan. Amma cikin ikon Allah yanzu kuma ga shi nan mun fara girban abin da muka shuka.”
High Chief Aminu Bizi ya ci gaba da bayyana cewa, ” Yanzu kusan shekara goma kenan kamfani na, na aiki kafada da kafada da CBN, wajen tallata manufofin Bankin CBN ga Al’ummar kasar nan, babu wani lungu da sako da ban shiga ba a kasar nan. Ni da ma’aikata mun sha wahala sosai, wani lokaci har ce mana akeyi Yan damfara, wani lokaci a ci zarafinmu, akwai lokacin da har tsaremu akayi, sai da aka kira daga sama sannan aka sake mu. Duk a dalilin irin wannan aikin na yanke zumunci da abokai da yan uwa, na fuskancin kalubale sosai, wanda ba kowa bane ke iya jurewa da hakan. Amma yanzu Alhamdulillah.”
Daga karshe Alhaji Aminu Bizi ya gode ma Bankin CBN a bisa wannan karamawa da suka bashi. Sannan ya mika godiyarsa ga daukacin ma’aikatan kamfanin Bizi Mobile baki daya. A cewarsa, wannan kambun lambar yabo nasu baki daya. A cewarsa.