Nijar Za Ta Bude Kan Iyakokinta Da Najeriya Yau Juma’a

IMG 20240322 WA0048(1)

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar a hukumance cewa, za ta bude kan iyakarta da Najeriya da misalin karfe 12 na tsakar daren yau.

Fiye da mako guda kenan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin bude kan iyakar da ke tsakanin kasashen biyu makwabtan juna, yayin da sojojin na Nijar suka ki cewa uffam kan matakin na Najeriya.

Kazalika shugaba Tinubu ya janye daukacin takunkuman karayar tattalin arzikin da Najeriya ta lafta wa Nijar.

Kan iyakar mai tazarar kilomita 1,600 ta ratsa jihohin arewacin Najeriya da suka hada da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina da Jigawa da Yobe da Borno.

A wani zama da ta gudanar a baya-bayan nan, kungiyar ECOWAS ta  amince da shirin cire wa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea takunkuman da aka dora musu sakamakon juyin mulkin soji da aka samu a cikinsu.

Masharhanta sun bayyana cewa, janye takunkuman da aka lafta wa Nijar, zai kawo saukin rayuwa ga al’ummar kasar da ke fama da tsadar rayuwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply