Ni Matar Manya Ce Na Fi Ƙarfin Yara – Mai Sa’a

Jarumar Kannywood kuma tsohuwar mai bada shawara ga Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Rashida Adamu Abdullahi wadda aka fi sani da suna “Mai Sa’a” ta bayyana wa duniya ita matar manya ce, ta fi karfin Yaro.

Jarumar ta bayyana haka ne yayin hirar ta da gidan Radio Freedoom Kano a yayin da aka tambaye ta kan matashin nan Musa Rafinkuka da yace yana sonta da aure.

Da aka tambayi jarumar ko ita ta yi wa Musa barazana har ya janye son da ya ce yana yi mata? Sai ta ce “ni ban tsorata shi ba amma na fada masa ruwa ba sa’an kwando bane”.

Ta ce “mun yi waya da shi ya fada min cewa shi masoyina ne tun yana yaro yake kallon fim dina shi ya sa ya rasa yadda zai isar da sakonsa sai ta wannan hanyar da ya bi”.

Ta ce “da na ji haka shine na nemi da ya yi bidiyo ya janye abinda ya fada akaina kuma har ya yi. Ni ba sa’ar yara bace. Ku kalle ni mana? Ni Mai Sa’a matar manya ce.

Meye Raayinku ?

Labarai Makamanta