Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya fito ya bayyana auren zobe da ke tsakanin shi da jam’iyyar PDP inda yace ce yana jin daɗin jam’iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam’iyyar APC kamar yadda Channels TV ya ruwaito.
A wata sanarwa da Gwamnan ya fitar ranar Juma’a ta hannun mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa Gwamnan na Bauchi na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam’iyya mai mulk ta APCi.
“Muna so mu sanar cewa wannan labarin karya ne da aka kirkira saboda wata bukata ta kashin kai, don jawo hankali masu bibiyar labaran siyasa wanda ficewar gwamnan Ebonyi ya sake ta’azzara labarin siyasar ƙasar,” a cewar Gidado.
Ya ƙara da cewa, “muna so mu sanar da cewa mai girma Gwamna Sanata Bala Mohammad bai taɓa kokonton barin PDP zuwa APC ba. “Sai dai, yanzu yana tsaka da cika alkawuran da ya ɗauka lokacin yakin neman zaɓe, wanda akan haka al’ummar Bauchi suka goya masa baya ya kifar da gwamnati mai ci.”
Saboda haka, gwamnan yana shawartar masoyansa sa, ƴan jam’iyyar PDP da al’ummar Bauchi da suyi watsi da rahoton. Ya kuma jaddada aniyarsa na inganta rayuwar al’umma mazauna Bauchi ba tare da nuna bambanci ba.